A wannan rana, jam'iyyar ta NSF ta kira taron shugabannin jihohi a birnin Alkahira. Kafin taron, mista El-Baradei ya bayyana wa kafofin yada labaru cewa, kamata ya yi Mohamed Morsi ya amsa kiran jama'a, wato yayi murabus daga mukaminsa, saboda mafi yawan jama'ar kasar Masar sun nuna rashin gamsuwa ga salon jagorancinsa.
Ban da haka, mista El-Baradei ya furta cewa, a sakamakon rashin manufofi masu kyau da Masar ke fuskanta karkashin jagorancin gwamnatin mai ci a yanzu, kasar na gamuwa da matsalolin tsanantar yanayin tattalin arziki, da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali, a sabili da haka, ana sanya ran samun canji. El-Baradei ya yabi kungiyar ta Tamarod, yana mai cewa, al'ummar Masar na share fage ga gwagwarmayar da za a shiga a ran 30 ga wata.
Kafin wannan, kungiyar fafitika ta Tamarod ta yi kira ga jama'ar kasar da su yi babbar zanga-zanga a ranar 30 ga wata, wato ranar cika shekara guda da kama aikin shugaba Morsi a matsayin sabon shugaban kasar, matakin da 'yan adawar ke fatan zai gaggauto da gudanar babban zaben kasar.
Domin mai da martani ga wannan mataki na 'yan adawa, bangare magoya bayan shugaba Morsi, sun riga sun yi zanga-zangar nuna gamsuwa da salon jagorancinsa a ranar 21 ga wata. (Fatima)