A Jiya Alhamis 4 ga wata, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Faransa ta ba da wata sanarwar kin yarda da rokon nasa.
Sanarwar ta ce, kamar yadda wasu sauran kasashe suka yi, ofishin jakadancin kasar Faransa dake kasar Rasha ta sami wata wasika daga wajen Edward Snowden domin neman samun mafakar siyasa a kasar. Amma, Faransa ta ki yarda saboda la'akari da shari'a da doka da kuma halin da Edward Snowden ke ciki.
Game da labarin da aka bayar na cewar Edward Snowden ya mikawa kasashe da dama ciki har da kasar Rasha wasikar rokon samun mafakar siyasa daga filin saukar jiragen sama na Sheremetyevo na kasar Rasha, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov ya mai da martani a wannan rana cewa, har yanzu bai sami roko daga Snowden ba tukuna.
Har wa yau babu tabbaci kan wurin da Snowden zai tafi ba. An ce, a halin yanzu, yana yankin matafiyan da ke kan hanyar su ta wucewa na filin saukar jiragen sama na Sheremetyevo dake birnin Moscow na kasar Rasha. (Amina)