A ran 1 ga wata, mambar kwamitin tsakiya na soja na jam'iyyar kwaminis ta Sin kana babban hafsan-hafsoshi janar Fang Fenghui wanda yake ziyarar aiki a kasar Rasha ya gana da babban hafsan-hafsoshin rundunar kasar Rasha janar Valeriy Gerasimov, inda suka yi shawarwari tare da zartas da takardar yin atisayen soja cikin hadin kai.
Valeriy Gerasimov ya shedawa manema labaru cewa, manyan atisayen soja har sau biyu da rundunonin kasashen Rasha da Sin za su yi a wannan shekara ta fuskar hadin kai wajen soja da siyasa sun hada da atisayen sojan jiragen ruwa da na sojan kasa.
Daga bisani kuma, Fang Fenghui ya sanar da cewa, za a yi atisayen soja a kan teku daga ran 5 zuwa 12 ga wata a Gulf Peterthe Great Bay a kan sararin tekun Japan, kuma za a yi atisayen soja cikin hadin kai don yaki da ta'addanci mai jigon "THE PEACE MISSION" daga ran 27 ga wata zuwa ran 15 ga watan Agusta a jihar Chelyabinsk ta kasar Rasha. Yana mai cewa, atisayen soja da rundunonin kasashen Sin da Rasha za su yi cikin hadin kai ba su shafi sauran kasashe ba, makasudin su shi ne domin zurfafa hadin kai tsakanin sojojin kasashen biyu da tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki. (Amina)