Mataimakin shugaban kasar Amurka ya bukaci shugaban kasar Ecuador da ya yi watsi da rokon Edward Snowden
Shugaban kasar Ecuador Rafael Correa ya bayyana a ranar 29 ga wata cewa, mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya tuntube shi ta wayar tarho a ranar 28 ga wata, inda Biden ya bayyana fatan Ecuador za ta ki amincewa da rokon Edward Snowden na shiga kasarta. Wannan ne karo na farko da aka gabatar da wannan batu a fili tsakanin manyan jami'an kasashen Ecuador da Amurka tun bayan da Snowden ya gabatar da rokon shiga kasar Ecuador.
Shugaba Correa ya ce, yayin da ake nazari kan rokon Snowden, kasarsa za ta yi la'akari da ra'ayin kasar Amurka. Amma ya jaddada cewa, kasartasa za ta tsaida kuduri a karshe kan rokon Snowden. (Zainab)