Ran 2 ga wata, kungiyar WikiLeaks ta sanar da cewa, ta riga ta gabatar da sabbin takardun neman mafakar siyasa a madadin Snowden ga kasashe guda 19, da suka hada da kasashen Jamus, Venezuela, Rasha da dai sauransu. Ya kara da kasashen Ecuador, Iceland, wadanda aka riga aka mika musu takardun a baya. Gaba daya Wikileaks ta gabatar da takardun ga kasashe 21. Amma ya zuwa daren ranar 2 ga wata, kasashe sama da 10 sun riga sun bayyana cewa ba za su amsa rokon kungiyar ba. Bugu da kari, saboda bai iya amince da bukatar da shugaba Vladimir Putin ya fitar cewa kada ya dauki karin matakan da za su kawo wa kasar Amurka matsaloli ba, Edward Snowden ya riga ya yanke shawarar janye takardar neman mafakar siyasa da ya gabatar wa kasar Rasha.
Ban da wannan kuma, ran 2 ga wata da dare, bisa agogon Moscow, shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro Moros ya tashi daga birnin Moscow. Bisa labarin da aka samu, an ce, har zuwa yanzu, Edward Snowden na zauna a filin jiragen sama na kasar Rasha. (Maryam)