130618murtala
|
A Najeriya ana shirin horas da 'yan sama jannati, domin aikin binciken sararin samaniya.
Yayin da yake gabatar da wani rahoto dangane da ci gaban da ma'aikatarsa ta samu a cikin shekaru biyu da suka gabata, a wajen wani taron manema labarai da aka yi a ranar Litinin a birnin Abuja, ministan ma'aikatar kimiyya da fasaha ta tarayyar Najeriya Prof. Ita Ewa, ya bayyana niyyar da gwamnati ke da ita, ta horas da wasu 'yan sama jannati domin yin zirga-zirga a sararin samaniya.
Prof. Ewa ya ce, ma'aikatarsa na jiran samun amincewar shirin daga shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, haka kuma yace, Najeriya zata hada kai tare da kasar Sin a fannin harba kumbo zuwa sararin samaniya.
Prof. Ita Ewa ya ce, an gina wata tashar harba kumbo, wadda ke da filin da ya kai tazarar kilomita 20 a Epe, jihar Lagos, kuma injiniyoyi 20 daga hukumar nazari da neman ci gaban sararin samaniya ta Najeriya wato NARSDA, suna kasar Sin suna samun horo kan wannnan aiki.
Prof. Ewa ya kara da cewa, idan shugaban kasa ya amince da shirin, Najeriya za ta fara shirin harba karin taurarin dan Adam na aikin sadarwa guda biyu.
Ya ce, harba tauraron dan Adam zai kawo alfanu ga kasar, musamman a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, ciki har da tabbatar da yanayin tsaro, da sa ido kan ambaliyar ruwa, da gurbatar muhalli, gami da kwararowar hamada, dama batun matsalar malalar mai a yankin Niger Delta.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.