Watan gajeriyar sanarwar da kakakin kungiyar Jomo Gbomo ya fitar bayan harin na ranar Asabar, ta bayyana kai harin a matsayin wani mataki na tirsasa gwamnatin kasar sakin daya daga jagororin kungiyar mai suna Henry Okah, wanda ba da jimawa ba aka yanke masa hukuncin dauri a kasar Afirka ta Kudu, bayan wata kotun kasar ta same shi da laifin aikata laifukan ta'addanci. Har ila yau cikin bukatun da kungiyar ta MEND ta bayyana, akwai saukar ministar man fetur ta tarayyar Nijeriyar Diezani Alison-Madueke daga mukaminta.
Gbomo ya ce, kungiyar ta MEND za ta ci gaba da kai makamantan wadannan hare-hare, har sai gwamnatin kasar ta biya dukkanin bukatun nasu. Tuni dai wani babban jami'in kamfanin man na NNPC ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya kuma ce, ana nan ana ci gaba da bincike.(Saminu)