Hakan ya biyo bayan sanarwar da hukumar 'yan sandan Birtaniya ta bayar na cewa sun kame karin mutane biyu, wadanda suke da alaka da harin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Mutanen biyu da aka cafke sun hada da wani namiji mai shekaru 29 da haihuwa, da wata mace mai shekaru 29 da haihuwa, amma ba'a bayyana sunayensu ba.
A cikin sakon nuna jaje da ya gabatar zuwa ga firaministan kasar Birtaniya David Cameron, gami da dukkanin jama'ar kasar, Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ita ma tana bakin-ciki sosai game da aukuwar wannan lamari.
Jonathan ya bayyana cewa, harin ta'addanci, hari ne da ke kawo barazana ga zaman rayuwar al'umma a kowace kasa, ya kamata jama'a na kabilu, addinai da yankuna daban-daban su hada kai domin yin Allah wadai da shi.
Shugaba Jonathan ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya tana kokarin hada gwiwa tare da gwamnatin Birtaniya da sauran kasashen duniya, domin yaki da duk wani nau'in ta'addanci.
A nasa bangaren kuma, firaministan kasar Birtaniya David Cameron ya kwatanta kisan wannan soja tamkar hari ne da aka kai kan Birtaniyar, kuma ya jaddada cewa kasarsa na yin tsayin daka wajen dakile ayyukan ta'addanci.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.