130521murtala
|
Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Afirka su lura da irin dimbin kudaden da ake fitarwa daga nahiyar Afirka ba bisa ka'ida ba.
Jonathan ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da wata tawagar dake kunshe da manyan masana a fannin kudaden da ake fitarwa daga nahiyar Afrika ta Majalisar Dinkin Duniya, a fadarsa ranar Litinin da ta gabata.
Shugaba Goodluck Jonathan ya jaddada cewa, dimin kudaden da ake fitarwa daga nahiyar Afirka, na iya warware matsalar da kasashen dake nahiyar ke fuskanta, musamman a fannin samarda ababen more rayuwar jama'a, dama ragowar fannonin ci gaba, don haka yace ya zama wajibi a tashi tsaye domin dakile wannan matsala.
Jonathan ya kara da cewa, kasashen Afirka na bukatar taimako daga kasashe masu arziki a wannan fanni, domin ta haka ne za'a iya rage yawan cin hanci da rashawa, musamman idan masu gudanar da wannan mummunar ta'ada suka rasa wuraren da zasu fidda haramtattun kudaden.
Bugu da kari, shugaba Goodluck Jonathan ya yi kira ga wannan tawaga ta MDD, da ta gudanar da bincike sosai kan wannan batu, ta kuma taimakawa kasashen Afirka wajen shawo kan wannan matsala.
Ya kuma bukaci dukkanin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin Najeriya da su bada cikakken hadin-kai ga wannan tawaga.
Cikin tsokacin tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, kana shugaban tawagar dake kunshe da manyan masana a kan kudaden da ake fitarwa daga nahiyar Afrika ta Majalisar Dinkin Duniya, Mr. Thabo Mbeki ya ce, Afirka tana yin hasarar kudaden da yawansu ya kai dala biliyan 50 a kowace shekara, saboda dimbin kudaden da ake kokarin fitar da su daga nahiyar, kuma tawagar zata lalubo bakin warware wannan matsala.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.