Shugaba Jonathan ya fadi haka ne a wajen wani taron gaggawa da aka yi jiya Jumma'a a fadar shugaban kasa wato Aso Rock Villa dake Abuja, babban birnin tarayya, inda ya gana da manyan jami'an tsaron kasar.
A jiya kuma, gwamnatin tarayyar Najeriya ta mayar da martani dangane da damuwar da gwamnatin kasar Amurka ta nuna kan kisan kiyashin da aka yi kwanan baya a garin Baga dake jihar Borno, inda aka sha alwashin cewa, za'a yanke hukunci mai tsanani kan duk wanda ya aikata laifin kisan.
A ranar Alhamis din nan ne, gwamnatin Amurka ta bukaci a gudanar da bincike sosai kan kisan kiyashin da aka yi ma fararen-hula a garin Baga na jihar Borno.
Bisa labarin da muka samu, an ce, a wajen taron da aka yi jiya, shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana matukar takaici da bacin-rai game da kisan da aka yi ma 'yan sanda a garin Bama na jihar Borno da kuma tashin-hankalin da aka yi a jihar Nassarawa, ya kuma bada umurni ga jami'an tsaro da su nemi ainihin dalilin da ya jawo barnar, da yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata laifi.
Manyan jami'an tsaro da suka halarci taron gaggawa a jiya, sun hada da, ministan harkokin 'yan sanda kyaftin Caleb Olubolade, babban mai bada shawara ga shugaban kasa kan harkokin tsaro Col. Sambo Dasuki, hafsan hafsoshi Admiral Ola Ibrahim, babban hafsan sojan sama Alex Sabundu Badeh, babban hafsan sojan ruwa Admiral Dele Ezeoba, da kuma specto janar din 'yan sanda, Muhammad Dikko Abubakar.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.