in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala aikin sanya murya cikin harshen Hausa kan fim "Soyayyar Matasan Beijing"
2013-06-14 17:15:42 cri

An yi bikin kammala aikin sanya murya da harshen Hausa kan wani wasan kwaikwayon telebijin na kasar Sin na farko mai suna "Labarin soyayyar matasan birnin Beijing" a yammacin ranar 13 ga wata a dakin daukan murya na gidan rediyon kasar Sin CRI, wanda ake sa rai za a gabatar da shi ga masu jin harshen Hausa a Afrika.

Mataimakin babban direkatan CRI Ren Qian ya halarci bikin tare da baiwa masu aikin sanya murya takardar yabo da wasikar nuna godiya.

Yana mai cewa, fitar da wasan kwaikwayo zuwa ga kasashen Afrika ya zama mataki mai kyau wajen yada al'adun kasar Sin, kuma hanya ce da ta dace wajen kara dankon zumunci dake tsakanin jama'ar bangarorin biyu. Ban da haka, ya jaddada cewa, kwarewar CRI kan harsuna da hanyoyin yada labarai ne ta taimaka ga aikin fassara wasan kwaiwayo.

An ba da labari cewa, masu aikin sanya murya 'yan Nijeriya guda shida za su koma kasarsu ba da jimawa ba.

Wakilin 'yan masu daukan murya Yahaya Babs ya nuna cewa, watanni biyu ke nan tun da aka fara aikin a tsakiyar watan Afrilu, kuma za a gabatar da wannan wasan kwaikwayo a karshen rabin wannan shekara a Nijeriya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China