in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude gidan rediyon CRI na 90 a kasar Georgia
2013-05-05 16:57:42 cri
A ranar 5 ga wata, an bude gidan rediyon kasar Sin CRI na 90 wato gidan rediyon Tbilisi a kasar Georgia a hukunce. Don haka yawan gidajen rediyon CRI a kasashen waje ya kai matsayin farko a duniya, kana yawan harsunan da gidan rediyon CRI ya ke amfani da su wajen gabatar da shirye-shirye ya kai 64, wannan ya tabbatar da matsayin CRI na gidan rediyon da ya fi kowanne yin amfani da harsuna daban-daban wajen gabatar da shirye-shirye a fadin duniya.

A wannan rana kuma, an bude gidan rediyon CRI na 88 wato gidan rediyon Amman a kasar Jordan, da kuma na 89 wato gidan rediyon Tirana a kasar Albania.

A 'yan shekarun da suka gabata, gidan rediyon kasar Sin CRI ya gaggauta gina gidajen rediyonsa a kasashen waje, kuma an bude gidajen rediyon 90 a manyan biranen kasashe 50 na nahiyoyi biyar a duniya, wadanda suka gabatar da shirye-shirye ga mutane kimanin miliyan 200. Kana ya kafa manyan cibiyoyin CRI guda 7 a nahiyoyin Afirka, arewacin Amurka, yammacin Turai, gabashin Turai, yankin gabas ta tsakiya, Asiya da kuma Latin Amurka tare da ofisoshin tsara shirye-shirye 22 a kasashen waje, wadanda suka taimaka wajen tsara da kuma gabatar da shirye-shirye a wurin. Ban da wannan kuma, an kafa ofisoshin 'yan jarida na CRI 32, kwalejin Confucius ta gidan rediyo 13, kungiyoyin masu sauraro 4115 a kasashen waje, kana yana gabatar da shirye-shirye na tsawon fiye da awoyi dubu 2 a kowace rana, kuma yana samun wasiku daga masu sauraro fiye da miliyan 3 a kowace shekara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China