An gudanar da bikin murnar cika shekaru 5 da kafa kwalejin Confucius na koyon Sinanci ta hanyar rediyo na CRI a nan birnin Beijing a ranar 14 ga wata, inda mataimakin shugaban babbar hukumar harkokin rediyo da telebijin na kasar Sin Li Wei, shugabar sashen koyon Sinanci na kasar Sin Xu Lin, wasu jakadun kasashen waje dake kasar Sin, direktoci daga kasar Sin da na kasashen waje na kwalejin, da yawansu ya haura 120 ne suka halarci bikin.
Shugaban gidan rediyon CRI Wang Gengnian ya yi jawabi cewa, an kafa kwalejin Confucius na koyon Sinanci ta hanyar rediyo ne don yada al'adun gargajiya da na zamani na kasar Sin, a matsayin wani kokarin hada al'adun Sin da na duniya ta wannan hanya.
A cikin shekaru biyar da aka kafa ta, kwalejin ta inganta koyar da darasi tare da inganta fasahohin gwada shirye-shirye, hada koyar da darasi da tsara shirye-shirye, horar da kwararru tare da yin amfani da su, da kuma yada al'adu tare da sada zumunta. Ta hakan ne kwalejin ta jawo hankali da kuma samun yabo daga kasashen da aka kafa ta.