An gudanar da bikin kaddamar da shirye-shiryen CRI a ofishin jakadancin kasar Sin dake Nouakchott a gaban idon jakadan kasar Sin dake kasar Mauritaniya Chen Gonglai, Mohamed Lemine Ould Moulay, sakatare janar na ofishin ministan sadarwa da hulda tare da majalisa na Mauritaniya.
Haka bikin ya samu halartar wata tawagar gidan rediyon CRI da wakilan kafofin watsa labarai na gwamnati da masu zaman kansu na Mauritaniya.
A cikin jawabinsa mista Chen Gonglai ya bayyana cewa, shirye-shiryen CRI daga birnin Nouakchott ya kasance wani aiki na tarihi. Haka kuma wani kashi ne na babbar dangantakar sada zumunci dake kasancewa tsakanin Sin da Mauritaniya. Musanyar al'adu za ta ci gaba da kawo babban taimako wajen karfafa fahimtar juna da abokantaka tsakanin al'ummomin kasashen biyu.
Har wa yau kuma, shugaban CRI mista Wang Gengnian ya isar da sakon taya murnar bikin, inda ya ce, bude gidan rediyon CRI na zangon FM a kasar Mauritaniya zai kawo sauki ga jama'ar kasar wajen fahimtar kasar Sin da ma duniya baki daya ta hanyar sauraren shirye-shiryen CRI, kana da taimakawa kasashen biyu wajen kara sada zumunci da mu'amala a fannonin siyasa, tattalin arziki, cinikayya da al'adu. (Maman Ada)