Mr. Xia Jixuan ya bayyana cewa, CRI na son hadin gwiwa tare da kafofin watsa labaru na kasashe daban daban, da kuma tattaunawa kan sabbin dabarun watsa labaru domin biyan bukatun jama'a na samun labaru.
Haka kuma ya kara da cewa CRI na dora matukar muhimmanci kan ayyukan watsa labaru a kasashen Afirka, kuma tana da aniyar hadin kai tare da kafofin watsa labaru na Afirka a fannonin shirye-shirye, cudanyar ma'aikata kana da yin intabiyu tare domin rage cikas da sassan biyu ke fuskanta wajen samun labaru a kasashen waje.
Mr. Xia ya ce, a matsayinsu na kasashe masu tasowa, kasar Sin da kasashen Afirka na da muhimmin nauyi a kansu, wato samar wa jama'a wani dandali don samun ra'ayi bai daya, a kokarin ciyar da zamantakewar al'umma da tattalin arziki kana da al'adu zuwa gaba.
Daya daga cikin 'yan tawagar, Mustafa Brutsch dake tare da gidan rediyon kasar Aljeriya ya zanta da wakilinmu, inda ya bayyana cewa, kafofin watsa labarun kasarsa sun fara watsa labarai zuwa kasashen waje kwanan nan tun da ba su wuce shekaru hudu ko biyar ba da farawa, don haka yana fatan samun damar hadin gwiwa tare da CRI ta wannan ziyara. A sa'i daya kuma, yana fatan koyon kyawawan sakamakon da CRI ya samu domin a kara fahimtar wata kasar Aljeriya a hakika.
Mahalarta wannan kwas din a kan aikin ilimin radiyo da talabijin 37 da suka ziyarci gidan radiyon CRI sun fito ne daga kasashen Aljeriya, Kamaru, kwaddibuwa, Nijar da sauran kasashen Afirka 11 masu amfani da harshen Faransanci.(Kande Gao)