in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Habasha sun tattauna kan dangantakar hulda
2012-06-18 11:05:44 cri
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sadu da firaministan kasar Habasha Meles Zenawi a ranar Lahadi 17 ga wata a Los Cabos na kasar Mexico, inda suka tattauna kan dangantakar hulda tsakanin kasashen biyu.

Shugabannin biyu sun sadu ne a daidai lokacin da za a soma taron kungiyar G-20 a ranar Litinin da Talata a Los Cabos, shahararren wuri ne ta fuskar yin yawon shakatawa.

Shi dai wannan taro zai mai da hankali kan maganar farfado da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, yayin da ake tinkarar matsalar tattalin arziki a kasashe masu anfani da sauran matsaloli.

Kasar Mexico da ta dauki nauyin gudanar da wannan taro, ta gayyaci kasar Habasha da wasu kasashen da ba su cikin kasashe membobi na kungiyar G-20 domin halartar taron na garin Los Cabos .

Kasar Sin da ta Habasha suna jin dadin huldar abokantakarsu ta dauri. A cikin 'yan shekaru na baya-baya nan, kasashen biyu sun karfafa huldarsu ta fannin siyasa kwarai da gaske ta hanyar tattaunawa da juna.

A cikin watan Agustan da ya gabata, firaminista Meles Zenawi ya yi ziyara a kasar Sin, abun da ya kara nuna wani sabon ci gaba na hulda tsakanin kasashen biyu.

Kasashen biyu na jin dadin huldar da ke tsakaninsu ta bangaren tattalin arziki da kasuwanci. Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar kasar Habasha ta fuskar kasuwancin, kuma ta fi zuba jari a Habasha bisa ga kasashen duniya.(Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China