in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farfado da dangantakar dake tsakanin Japan da Zimbabwe na da alaka da ma'adinnai
2013-06-03 15:53:42 cri

Kafofin yada labarai na kasar Zimbabwe sun ba da labari a ran 2 ga wata cewa, gwamnatin kasar Japan tana daukar halin ko-in-kula kan kasar Zimbabwe, amma kwanan nan ta fara kokarin farfado da dangantakar dake tsakaninta da kasar Zimbabwe, kuma dalilin haka shi ne tana son shiga aikin hakar ma'addinai na kasar.

Labarin ya ce, firaministan kasar Japan Abe Shinzo ya gayyaci shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da ya halarci taron kasa da kasa na raya nahiyar Afrika karo na biyar da aka yi a kasar Japan tare kuma da yin shawarwari da shi, jami'an kula da harkokin man fetur, gas da ma'adinnai na kasar Japan bayan da suka gana da Mugabe sun bayyana burinsu na shiga aikin hakar ma'addinai a kasar Zimbabwe.

An kara da cewa, z yanzu haka, Japan tana shigo da wasu ma'addinai daga Zimbabwe, amma bayan wannan, tana kuma fatan zurfafa hadin gwiwa har ta shiga aiki na hakar ma'adinai kai tsaye. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China