Al'ummar kasar Zimbabwe za su kada kuri'ar raba gardama, kan daftarin sabon tsarin mulkin kasar a ran 16 ga wata, domin share fagen zaben shugaban kasar da za a yi, inda ya zuwa yanzu ake ci gaba da shirye-shirye yadda ya kamata.
Shugaban gudanarwa na hukumar zaben kasar Joyce Kazembe, ya nuna cewa, yanzu haka an isar da kayayyakin da za a yi amfani da su wajen kada kuri'un, zuwa tasoshi 9449 karkashin kyakkyawar kareya,domin ba da tabbaci ga aikin da za a yi a ranar 16 ga wata. Ban da haka, hukumar ta horar da wasu ma'aikatan gwamnati, domin tabbatar da doka da oda, yayin kada kuri'u. Har ila yau, kafofin yada labarun kasar, sun a kokarin wayarda domin wayarda kan al'umma muhimmancin wannan lamari, tare kuma da yin kira ga jama'ar da su kada kuri'u bisa ra'ayin su, tare da yin la'akari da makomar kasar. (Amina)