in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Shugaban Zimbabwe ya sa hannu kan sabon kundin tsarin mulki
2013-05-23 10:30:59 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sa hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar laraban ran 22 ga wata, abin da ya kawar da wani babban cikas ga babban zabe da za a yi cikin wannan shekara. Hakan ya sa an kammala aikin gyara kundin tsarin mulki, sai dai ba a gabatar da hakikkanin lokacin da za'a yi zabe ba.

Manazarta na ganin cewa, wannan sabon kundin tsarin mulki ya kayyade mulkin shugaban kasar, wanda kuwa ya baiwa ministocin gwamnati karin karfi, kuma ya tanadi cewa, wa'adin shugaba ba zai wuce biyu ba wato shekaru goma ke nan. Ban da haka, ya yi amfani wajen gyara da bada tabbaci kan hakkin jama'a da tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata da dai sauransu.

Dadin dadawa, zartas da wannan sabon kundin tsarin mulki ya samar da wani yanayi mai kyau ga zaben shugaba da majalisu da gwamnatocin wurare daban-daban da za a yi cikin wannan shekara. Ya zuwa yanzu, babu tabbaci game da hakikkanin lokacin yin zabe, manyan jam'iyyu biyu kowane ya nace ga matsayin sa.

Hakan ya sa wasu manazarta sun bayyana cewa, saboda an karato karshen wa'adin 'yan majalisu a wannan karo nan da karshen watan Yuni, kuma akwai ayyuka masu wuya da dama da za a yi wajen share fagen babban zabe, hakan ya sa zai yi wuya a gudanar da zabe a karshen watan Yuni. Ban da haka, an yi kididdiga cewa, ana bukatar dala miliyan 130 domin gudanar da babban zabe, abin da kuma zai yi wuya a samu wadannan kudi bisa halin da ake ciki a kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China