A yayin taron, kwamishinan kula da samar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU Ramtane Lamamra ya bayyana cewa, nahiyar Afrika na fuskantar kalubale da dama wajen kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa mai karko, kuma a kan samu rikici da ta'addanci da 'yan fashin teku da yin laifuffuka na ketaren kasashe da kuma juyin mulki. Ban da wannan kuma, nahiyar Afrika ba ta kware ba wajen kiyaye zaman karko na kasashenta, sabo da haka, ya yi kira ga hukumomin lekan asiri da na harkokin tsaro na kasashe daban-daban na Afirka da su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu, domin inganta kwarewarsu don warware rikici.
A yayin bikin bude taron, shugaban kasar Zimbabwe Gabriel Mugabe ya yi jawabin fatan alheri, inda ya bayyana cewa, tun daga shekarar 1990, an samu manyan rikice-rikice a kalla sau 20 a nahiyar, kuma abin da ya kawo babbar hasara wajen tattalin arzikin nahiyar, kuma ya kawo hujjar kasancewar sojojin kasashen yammacin duniya a nahiyar. Haka kuma, Mugabe ya sake zargin kasashen yammacin duniya da canja ra'ayoyin kungiyar kasa da kasa, don kawo hujjar daukar matakin soji a nahiyar Afrika, kuma ya ce, dalilin da ya sa suka yi hakan shi ne, don kwace albarkatun ma'adinai na nahiyar.(Bako)