in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Zimbabwe zata karbi bakuncin taron bitar FIFA a Harare
2011-09-16 10:00:35 cri
A wani kokari na kara cusa ra'ayin kwallon kafar mata a tsakanin al'umma da wadanda harkar ta shafa, kasar Zimbabwe zata karbi bakuncin wani taron karawa juna sani na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a cikin watan Nuwamban bana.

Ranar Alhamis din nan ne gidan rediyon kasar Zimbabwen ya ambato Florie Ramogodi, jami'ar kula da ayyukan musamman ta hukumar FIFA tana cewar, al'amarin na yini hudu da hukumar kwallon kafa ta kasar Zimbabwe ZIFA, ta shirya kuma ya samu tallafin kudi daga hukumar FIFA, zai gudana ne a Harare babban birnin kasar daga ran daya zuwa ta hudu ga watan Nuwamban.

Hukumar kwallon kafa ta duniyar, zata yi kokarin fadakarwa ne kan yadda za'a samar da alfanu daga harkokin wasannin 'yan mata.

Ramogodi wadda ta fito daga ofishin bunkasa harkokin wasanni na FIFA dake birnin Gabrone na kasar Botswana, ta gana da jami'an hukumar ZIFA, da sauran wadanda harkar ta shafa don duba yadda Zimbabwe ta kai wajen samar da kayayyakin da ake bukata don gudanar da wannan gagarumin taro.

Taron bitar zai samu halartar masu gabatar da takardu daga kungiyoyin FIFA na cikin kasar da kuma kafofin yada labarai. Inda za'a duba yanayin bunkasar kwallon kafar mata, da matsayin da take ciki, irin alfanun da zata iya samarwa da dai makamantan hakan. (Garba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China