Idan wannan kundi ya samu karbuwar jama'a, shi ne zai maye gurbin wanda aka zana kafin kasar wadda ke kudancin Afirka ta samu 'yancin kai a shekarar 1980, kuma shi ne zai share fagen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa nan gaba a cikin wannan shekara.
Wannan shi ne karo na biyu a yunkurin canza kundin tsarin dokokin kasar ta Zimbabwe. A shekarar 2000, ba'a cimma nasarar yin canjin ba saboda mafi yawan masu kuri'a sun yi watsi da batun cewa an baiwa shugaban kasa iko fiye da kima.
Ya zuwa yanzu hukumar zabe ta kasar Zimbabwe ta dau sunan masu sa ido na ciki da wajen kasar kusan dubu biyu wadanda za su yi aikin duba yadda kuri'ar raba gardaaman ke gudana.
Hukumar zaben ta samar da cibiyoyin zabe guda dubu 9,456 sannan ta nada jami'ai guda dubu 56,736 don gudanar da zaben raba gardaman.
Hukumar zaben ta ce za'a sanar da sakamakon nan da kwanaki biyar. (Lami Ali)