Lokacin da ya ke jawabi a taron yaki da cutar kanjamau na kasa, Mugaba ya ce ya zama wajibi a yiwa dukkan mata masu juna biyu da mazajensu gwajin cutar.
Kafar yada labarun kasar New Ziana ta ruwaito shugaban yana cewa, hakika zai fi dacewa idan ma'aurata suka san matsayinsu dangane da cutar kafin su haihu. Inda ya ce idan mace mai juna biyu ta san cewa tana dauke da cutar, hakan zai taimaka mata wajen shan maganin da ke rage kaifin cutar don lafiyarta da kuma na jaririn da ta ke dauke da shi.
Shugaba Mugabe ya ce, wannan mataki zai taimaka wajen hana sabbin masu kamuwa da cutar tare da hana yaduwar ta ga yaran da ba a haifa ba. Kuma hakan na iya samar da al'ummar da ba cutar kanjumau a cikinta. (Ibrahim)