in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Zimbabwe za ta fara samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da shara
2012-04-11 11:35:36 cri

Kasar Zimbabwe za ta kulla kawance domin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da shara a cibiyar sarrafa shara ta Firle da kuma Crowborough da ke Harare, babban birnin kasar, kamar yadda majalisar birnin ta sanar.A cikin wata hira ta kafar watsa labarai a ranar Talata, kwamitin tattalin arziki na majalisar ya sanar da cewa, akwai babbar ma'ana ga yin aiki da iskar gas domin samar da wutar lantarki ta ingantacciyar hanya don kawar da hadarin da mahalli ke ciki. Samar da wannan wutar zai magance gurbacewar muhalli da kuma dogaro kan hukumar ZESA kamar yadda aka sanar a karshen hirar. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China