in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai makoma mai haske game da samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a cikin shekaru 20 masu zuwa
2013-01-08 15:33:54 cri
Ranar 7 ga wata an kira taron nazarin yanayin makomar tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2013, a birnin New York, inda tsohon mataimakin babban shugaba kuma masanin tattalin arziki na farko na bankin duniya, kuma farfesa a jami'ar Peking Lin Yifu, ya nuna cewa, yana da imani sosai ga makomar tattalin arziki, kuma a ganin sa, Sin za ta samu ci gaba mai kyau wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin cikin shekaru 20 masu zuwa.

Lin Yifu ya ce, akwai makoma mai haske ta fuskar raya sana'o'i da manyan gine-gine a kasar Sin, ya ce idan Sin ta ci gaba da yawaita rinjayen da take da shi, za ta iya samun bunkasuwa da sauri wajen tattalin arziki. Ban da haka, ya yi kiyasin cewa, cikin 'yan shekaru masu zuwa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasuwa da kashi 8 bisa dari a kowace shekara.

A sa'i daya kuma, farfesa Lin Yifu, ya ce idan aka yi hangen nesa, Sin na fuskantar manyan kalubaloli biyu, wato matsalar da mutane masu matsakaicin kudin shiga ke fuskanta, da karuwar yawan tsoffi. Duk da haka, shugabannin kasar na fahimtar kalubalolin da ake fuskanta sosai, kuma ya yi imani cewa, Sin za ta ci gaba da bin hanyar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje wadda take bi cikin shekaru 30 da suka wuce, tare da tinkarar kalubaloli da kasashe masu tasowa suke fuskanta domin canja hanyar da suke bi dangane da raya tattalin arziki. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China