Mr. Angel Gurria ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin a hedkwatar OECD dake birnin Paris na kasar Faransa. Ya kuma yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai karu tsakanin kashi 7.5 cikin dari da kashi 7.7 cikin dari a bana, sannan zai karu da kashi 8 cikin kashi dari a shekarar 2014, kuma zai ci gaba da samun ci gaba da dorewa cikin shekaru 50 masu zuwa.
Mr. Angel Gurria ya kara da cewa, har yanzu maganar tattalin arziki batu ne da ke jawo hankalin kasa da kasa. Wasu sabbin kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin za su ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri cikin shekaru masu zuwa, kuma mai yiyuwa ne nan da shekaru 50 masu zuwa, za su wuce kasashe mambobin kungiyar OECD, hakan zai canja halin da ake ciki ta fuskar tattalin arzikin kasa da kasa gaba daya. (Sanusi Chen)