in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana zai iya zarce kashi 7.5%
2012-10-26 17:25:19 cri
Bisa la'akari da wasu abubuwan da suka shafi fannoni daban daban na tattalin arziki, an yi hasashen cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana zai iya zarce kashi 7.5%.

Yu Bin, darektan sashen nazarin harkokin ci gaba na majalisar gudanarwa ta kasar Sin shi ne ya yi wannan furuci a ranar 26 ga wata. Bisa ga alkaluman tattalin arzikin da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar a wannan wata, a farkon watanni 9 na wannan shekara, yawan GDP da aka samu a kasar Sin ya zarce kudin Sin yuan biliyan 35000, wanda ya karu da kashi 7.7%. Amma idan aka yi nazari, za a gano cewa, yawan karuwar a farkon watanni uku ya kai kashi 8.1%, a yayin da adadin ya kai kashi 7.6% daga watan Afrilu zuwa Yuni da kuma kashi 7.4% daga watan Yuli zuwa Satumba, abin da ya shaida wata alamar raguwar saurin bunkasar tattalin arzikin. A game da damuwar kasa cimma burin samun kashi 7.5% na bunkasuwar tattalin arziki, Mr.Yu Bin ya yi nuni da cewa, sakamakon manufofin kudi masu sassauci, tattalin arzikin duniya na samun farfadowa cikin gajeren lokaci, lamarin da ya sa kayayyakin da kasarmu ke fitarwa zuwa kasashen ketare za su fara karuwa sannu a hankali. Ana sa ran samun bunkasuwar tattalin arziki da ya kai kashi 7.5%, amma ga alama yawan bunkasuwar zai kai fiye da kashi 7.5%.

Yu Bin ya kara da cewa, yawan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekara mai zuwa zai yi daidai da na wannan shekara. Yu Bin yana kuma ganin cewa, ta yin la'akari da raguwar zuba jari da hauhawar farashin da za a iya fuskanta a shekara mai zuwa, ya kamata gwamnatin kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da manufofin kudi masu inganci.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China