Rahoton ya kuma bayyana raguwar adadin hajojin da Sin ta fitar, da kuma raguwar farashin kudin gidaje cikin shekarar 2012 wadanda suka haddasa raguwar saurin habakar tattalin arziki, amma duk da hakan, yanayin tattalin arzikin kasar ya farfado a karshen shekarar ta bana.
Haka zalika rahoton nan ya bayyana cewa, saboda wannan raguwa ta saurin karuwar tattalin arzikin kasar ta Sin, adadin karuwar tattalin arzikin yankunan Asiya ta gabas na shekarar 2012 ba zai haura na shekarar 2011 ba, sai dai adadin zai karu cikin shekarar 2013 mai zuwa. Bugu da kari, rahoton ya ce, akwai kalubaloli da dama wadanda watakila za su haddasa illa ga karuwar tattalin arzikin yankunan Asiya ta gabas, cikin su, har da gyare-gyaren manofofin yankuna masu amfani da kudin Euro na Turai, da babbar matsalar bashin da Amurka ke fama da ita, da kuma matukar raguwar adadin kudaden zuba jari na Sin, da dai sauran matsaloli. (Maryam)