in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar tattalin arzikin Sin tana raguwa sannu a hankali, a ganin IMF
2012-07-25 14:50:24 cri
Asusun bada lamuni na duniya wato IMF da cibiyarsa ke birnin Washington dake kasar Amurka ya bayyana a ranar 24 ga wata da cewa, ko da yake ana kara tsananta hadarin tattalin arziki na duniya, amma bisa kididdigar da aka bayar, an ce, karuwar tattalin arzikin kasar Sin tana raguwa sannu a hankali.

A kwanakin baya, asusun na IMF da kasar Sin sun kammala shawarwari kan aya ta hudu dake cikin ka'idojin IMF, inda daga baya suka gabatar da wani rahoto. Asusun IMF ya kiyasta cewa, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar Sin a bana zai karu da kashi 8 cikin kashi dari, kuma yawansa a shekara mai zuwa zai karu da kashi 8.5 cikin kashi dari.

Asusun IMF ya nuna cewa, a sakamakon raguwar farashin kayan abinci, an samu sassaucin matsalar da aka fuskanta sakamakon hauhawar farashin kaya a kasar Sin. Muddin ba a fuskanci wata matsala wajen samar da amfanin gona ba, yawan hauhawar kaya na kasar Sin a bana zai kai kashi 3 cikin kashi dari zuwa kashi 3.5 cikin kashi dari. Ana sa ran cewa, yawansa a shekarar 2013 a kasar zai kai kashi 2.5 cikin kashi dari zuwa kashi 3 cikin kashi dari.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China