Jiya Laraba 29 ga wata, jami'in rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Cote D'ivoire UNOCI ya shedawa manema labaru cewa, UNOCI da rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Liberia UNMIL sun hada kai domin dukufa kan kiyaye zaman lafiya a kan iyakar kasashen biyu.
Mataimaki mai ba da jagoranci na UNOCI ya ce, UNOCI da UNMIL sun tsai da shirin yin aiki tare, kuma za su dukufa kan kiyaye zaman lafiya da yankin dake ba da kulawa. Kuma za su yi atisayen soja cikin hadin kai a ko wane wata, musamman ma a fannin sararin sama, da kuma ba da tabbaci ga samar da jirgin sama mai saukar unguru.
An ce, an kawo karshen rikicin bayan babban zabe a kasar Cote D'ivoire, inda aka samu barkewar rikice-rikice a yammacin kasar, musamman ma a wasu garuruwa dake kan iyakar kasar Cote D'ivoire da Liberia. Gwamnatocin kasashen biyu sun yanke shawarar hada kai domin daidaita wannan matsala tare. (Amina)