in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ta samu damar shiga gasar cin kofin Afirka
2012-10-14 17:48:17 cri
Ranar Asabar 13 ga wata, kungiyar kwallon kafa ta kasar Nijeriya 'Super Eagles', ta lashe kungiyar kasar Liberia, nasarar da ta bata damar shiga gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2013 da kasar Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncinta.

A yayin wannan wasa da ta gudana a tsakanin kungiyoyin kasashen Nijeriya da Liberia a filin wasannin U.J Esuene na birnin Calabar dake kudu maso gabashin kasar Najeriya, Nijeriya ta lashe Liberia da ci 6 da 1.

Kafin karawar, kungiyoyin 2 sun buga kwallo a Monrovia na kasar Liberia, inda suka yi kunnen doki 2 da 2. Nasarar da Najeriya ta samu a wannan wasa da aka buga ta tabbatarwa Nijeriya samun damar shiga gasar kwallon kafa da ta fi muhimmanci a nahiyar Afirka, wato gasar cin kofin Afirka mai zuwa da za'a shirya a Afrika ta Kudu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China