A cikin wata sanarwar da ya zo hannun kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua a yau Talata 28 ga wata, an ce bangarorin biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ne a ofishin bankin Duniyar dake birnin Washington na kasar Amurka, kuma jakadan kasar Liberiya a kasar Amurka Jeremiah Sulunteh da mukaddashin mataimakin shugaban bankin mai kula harkokin nahiyar Afrika, Shantayaan Devarajan su ne suka rattaba hannun.
A lokacin bikin Jakada Jeremiah Sulunteh ya ce wutan lantarki na daya daga cikin manyan matsalolin dake fuskantar farfadowar tattalin arzikin kasar Liberiya kuma wannan aiki da za'a yi zai taimaka wajen yin kwaskwarima da kuma cigaban kasar.
A nasa bangare, Shantayanan Devarajan, ya ce shirin samar da wutar lantarki na WAPP na nuna yadda kasashe da hukumomin kasashen duniya za su iya hada kansu wajen amfani da wutan lantarki tare da kuma cigaba da ayyukan more rayuwan jama'a daga tsallaken kasashe. Tare da tallafin bankin raya kasashen Afrika, bankin zuba jari na kasashen Turai EIB, da wani kamfani na kasar Jamus KFW, sannan da gwamnatocin kasashen hudu, aikin farko na wannan yarjejeniyar zai dauki nauyin a kalla kilomita 1,349 da zai hada kasashen Kwaddibuwa, Liberiya, Sierra leone da kuma Guinea.
Wannan aiki yana la'akari da kasashen yankunan Saharan da suke farfadowa daga tashe tashen hankula kuma ake masu kallo wadanda suka fi sauran kasashen duniya talauci. Yanayin wutan lantarki a kasar Liberiya, Sierra Leaon da kuma Guinea su ma suna da bukatar a duba su don yi masu gyaran fuska da kuma fadada su.