in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jami'ar MDD ta nuna yabo ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake Liberia
2012-10-14 17:48:17 cri
Wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD, kana mai shiga tsakani kan batun Liberia ta MDD, Karin Landgren ta nuna yabo ga wata rundunar kasar Sin na tawagar UNMIL dake Zwedru, wadda ta taimakawa kasar Liberia wajen samar da kuma kiyaye manyan kayayyaki na amfanin jama'a a kudancin kasar.

"Wannan ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta ba da agaji tare da cika alkawarinta yadda ya kamata. Wadannan hanyoyi da gadojin da sojojin kasar Sin suka gina suna taimakawa yara wajen zuwa makarantu, yayin da suka taimakawa masu ciniki wajen jigilar kayayyakinsu zuwa kasuwanni, tare da ba da damar samun hidimomi, kamar zuwa cibiyoyin kiwon lafiya, ofishin 'yan sanda da dai sauransu. Duk wadannan sun taimakawa kasar Liberia wajen samun ci gaba da bunkasuwa." A cewar Karin Landgren.

Ban da haka, bisa wani labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar a jiya ranar 13 ga wata, madam Landgren ta yi wannan kalami a yankin Zwedru na gundumar Grand Gedeh a ranar Juma'a, inda ta kuma yaba da kokarin rundunar jigilar kayayyaki ta kasar Sin dake cikin tawagar UNMIL.

Dadin dadawa, madam Landgren ta nuna yabo ga rukunin likitoci na kasar Sin dake aiki a wani asibiti a yankin Zwedru, wanda ya tabbatar da lafiya da kuma alheri ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, tare da kula da lafiyar jama'a dake wurin.

Madam Landgren ta kara da cewa, ci gaban kasar zai kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin. Yanzu tawagar UNMIL na iya mai da hankali kan mika nauyin dake kanta na kiyaye tsaro ga gwamnatin kasar a kai a kai. Amma kuma, wannan ba ya nufin cewa, tawagar UNMIL za ta janye jikinta nan take ba.

"Abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Liberia. Tawagar na hadin gwiwa tare da mahukuntan kasar, kamarsu ofisoshin 'yan sanda, hukumomin tsaro da sauransu, ta yadda za a tabbatar da cewa, wadannan hukumomi na da isasshen karfi wajen sauke nauyin dake kansu na kiyaye tsaro da zaman lafiyar kasar." In ji madam Landgren. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China