A cewar shugaban tawagar kasar Liberiya Alfred Koiwood, wannan wata manufa ce ta fahimtar halin da ake ciki a wurin, ta yadda 'yan majalisar dokokin kasar Liberiya za su ba da umurnin fitar da kudaden da za'a kashe wajen karfafa tsaro a kan yankin iyakar kasashen biyu.
Ministan cikin gida na kasar Cote d'Ivoire Hamed Bakayoko ya bayyana gamsuwarsa kan irin wannan hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna musammun kan batun tsaro. Yankin kan iyaka tsakanin kasashen biyu ya kasance wani dandalin tashe-tashen hankalin zubar da jini sau da dama da wasu mutane dauke da makamai suka aikata dake fitowa daga kasashen biyu. (Maman Ada)