A lokacin taron hadin gwiwwa karo na biyu na kungiyoyi masu yaki da cutar da yanzu hakan ake yi a Grand Bassa, wani yanki dake gabashin kasar, shugaban shirin yaki da cutar ta SIDA, Sonpon Blamo Sieh ya bayyana cewa, jami'an kiwon lafiya sun samu masu dauke da cutar 13,992 a tsakanin watan Afrilun shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2012.
Mr Sieh ya ce, gwamnati ta bullo da shiri daban daban don tabbatar da rage yawan yaduwan wannan cuta, wanda ya hada da samar da isassun bayanai da fadakarwa a fadin kasar da kuma samar da wadatattun kororon roba don tabbatar da jima'i mara hadari.
Ya ce, kusan cibiyoyi 30 na gwaji tare kuma da karban magani na cutar ta SIDA yanzu haka aka bude a fadin kasar da yake da masu dauke da cutar 13,992 kuma 10,662 na karban maganin rage karfin cutar a jiki, haka kuma wannan adadi a cewar shi na nuna yawan masu dauke da cutar a matsayin miliyan 3.5, abin da yake kasa in aka kwatanta shi da wassu kasashe a Afrika. (Fatimah)