A matsayinsa na shahararren dan siyasa a kasar, tsohon shugaba Blah ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar a gwamnatin shugaba Charles Taylor, kafin daga bisani ya kasance shugaban kasar na tsawon watanni biyu, sakamakon murabus da Charles Taylor din ya yi daga mukaminsa. Ya kuma sauka daga matsayin shugabancin kasar a ranar 14 ga watan Oktobar shekarar 2003 bayan kafa gwamnatin rikon kwarya da MDD ta marawa baya.
An dai haifi marigayi Blah ne a ranar 18 ga watan Afirilun shekarar 1947, ya kuma rasu yana da shekaru 66 a duniya. (Saminu Hassan)