Ya yi bayanin cewa, za a yi amfani da wadannan kudade wajen raya wani babban aikin da ya shafi majalisar ministocin kasar Liberiya, da girmama fadin cibiyar horar da sana'o'i ta Monrovia ta kasar, sannan kuma da fadada ginin majalisa dokokin kasar.
Augustine Ngafuan, ministan harkokin wajen kasar Liberiya, a madadin shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kasar, shine ya sa hannu a kan wannan yarjejeniya tare da Zhao Jianhua, a matsayinsa na wakilin gwamnatin kasar Sin a ranar Jumma'a da ta gabata.
Ta wadannan matakai, kasar Liberiya ta bayyana burin jama'arta, Augustine Ngafuan ya fadi haka ne a gaban wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin bayan da ya sa hannu a kan wannan yarjejeniya.
Zhao Jianhua, jakadan kasar Sin da ke kasar ya nuna farin cikin sa na ganin an rattaba hannu a kan yarjejeniyar,inda ya ce, kasar Liberiya ta samu manyan nasarori wajen farfado da ayyukan kasar daga dukkan fannoni, a karkashin jagorancin shugaba Ellen Sirleaf.
Haka kuma inji shi wannan wani kyakkyawan abin shaida ne da ganin yadda Liberiya ta samu ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma bisa goyon bayan gwamnatin kasar Sin. A don haka Sin na sa ran ganin kyakkyawar makomar kasar Liberiya a nan gaba.(Kande Gao)