Dokar zaben kasar Liberia ta ce dole ne dan takarar shugaban kasa ya samu kashi 50 cikin 100 kana kuma da kuri'a guda daya cikin wanda aka kirga kamar yadda sharadi na 83b na kundin mulkin kasar na 1986 ya gindaya.
A taron manema labaru yammacin talatan nan,shugaban hukumar zaben James Fromayan yace ba'a cika sharuddan ba lokacin zaben da ya gabata don haka za'a yi zaben raba gardama a ranar 8 ga watan gobe wato nuwamba.
A ta bakin Mr Fromayan,za'a gudanar da zaben raba gardama tsakanin 'yan takara biyu da suka fi samun kuri'u wandanda suka hada da Ellen Johnson-Sirleaf na jam'iyyar Unity Party da kuma Winston Tubman na jam'iyyar Congress of Democratic Change.(Fatimah)