in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun yi alkawarin baiwa kasar Mali tallafin kudi Euro biliyan 3.25
2013-05-16 10:37:25 cri

An gudanar da taron kasa da kasa dangane da baiwa kasar Mali tallafi a birnin Brussel hedkwatar kasar Belgium, bangarori daban-daban da wannan abin ya shafa ciki hadda kungiyar EU sun yi alkawarin baiwa kasar Mali tallafin kudi da yawansa ya kai Euro biliyan 3.25 domin taimaka mata wajen farfado da kasar.

EU, Faransa da Mali ne suka hada kai domin gabatar da wannan taro mai jigon "Hadin kai domin samar da wata sabuwar Mali". A cikin wata sanarwa da aka bayar bayan taron, an ce, mahalarta taron sun yi wannan alkawari ne bisa kasafin kudi da aka yi cikin wani shirin farfado da kasar cikin dogon lokaci da gwamnatin kasar Mali ta gabatar daga shekarar 2013 zuwa 2014.

Shugaban rikon kwaryar kasar Mali Dioncounda Traore ya nuna cewa, taimakon da kasashen duniya za su bayar zai sa kaimi ga kokarin farfado da tattalin arziki da al'ummar kasar Mali, har ma zai taka rawa wajen inganta yanayin tsaro da maido da zaman doka da oda. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China