in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mukadashin shugaban majaliasar dokokin kasar Mali ya yi kira da aiwatar da shirin mika mulki
2013-04-02 10:25:38 cri
Mukadashin majalisar dokokin kasar Mali, Younoussi Toure, ya sanar a ranar Litinin a yayin bude zaman taron majalisar na watan Afrilu, cewa zabubuka masu zuwa za su kasance wani ginshikin zaman lafiya da na karko musammun ma idan wadannan zabubukan sun shafi fadin kasar baki daya.

Kasashe abokai sun zo sun taimake mu, babu shakka. Amma domin tashi tsaye, ya kamata mu da kanmu mu nuna niyyar tashin tsaye. Kuma tashin tsayenmu shi ne na aiwatar da shirin mika mulki ba tare da kasala ba, matakin farko ga girmama kalandar da aka tsaida da kuma shugaban kasa ya rike domin gudanar da wadannan zabubuka a cikin watan Yulin shekarar 2013, in ji mista Toure.

Mista Younoussi Toure ya bayyana cewa ya kamata tutar kasar Mali ta rika kadawa a ko'ina cikin kasar daga Kayes zuwa Kidal, wannan na nufin cewa za'a sake tura hukumomi a cikin wadannan yankuna da aka kwato, kuma na nufin cewa za'a shirya aikin maido da al'ummomin da suka fice ko gudun hijira daga yankunansu.

A lokacin da yake tabo maganar maida tawagar kasa da kasa ta taimakon kasar Mali (MISMA) a matsayin tawagar sojojin wanzar da zaman lafiya ta MDD, mista Toure na ganin cewa ya kamata tawagar ta kasance cikin tsarin yaki da ta'addanci da kuma karfafa karfin rundunonin sojojin da aka tura fagen daga. Kuma hakan zai gaggauta kawo gyaran fuskar rundunar sojojin kasar Mali ta yadda za ta samu karin mutane da kuma kayayyakin aiki ga sansanoninta.

Hakazalika mista Toure ya bayyana cewa kafa kwamitin sassanta 'yan kasa da kuma fara aikinsa wani mataki ne mai muhimmanci.

A yayin bude zaman taro wannan majalisa, an samu halartar tawagogin 'yan majalisun kasashen Cote d'Ivoire, Nijar, Burkina-Faso, Cadi da kuma Senegal. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China