A halin da ake ciki kuma masu aikin jin kan bil adama na MDD a kasar sun yi gargadi cewa akwai matsalar karancin abinci a kasar ta yammacin Afirka ga kuma rashin isassun kudade a asusun gudanar da aikin ba da tallafi na kasa da kasa.
Ofishin MDD a kasar Mali (UNOM) ya yi suka cikin wata sanarwa bayan harin da aka yi a Kidal dake yankin arewa maso gabashin kasar cewa MDD ta yi tir da harin bom da aka kai wanda ya yi rauni ga dakaru da dama dake aiki karkashin AFISMA.
Sanarwar ta ci gaba da cewa wannan hari ko kadan ba zai hana MDD ba da goyon baya ga dakarun na AFISMA ba a yunkuri da suke na maido da zaman lafiya da iko a kasar Mali. (Lami Ali)