Gwamnatin kasar Mali ta bayyana cewa, an kara yawan kasafin kudin kasar na shekara ta 2013 daga cefa 1,007 wato kimanin dala biliyan 2 a tun farko zuwa sefa biliyan 1,433 kimanin dala biliyan 2,87, inda aka samu karin kashi 42.3 cikin 100 ke nan.
Shugaban rikon kwaryar kasar Mali Diocounda Traore ne ya bayyana karin kasafin kudin, bayan ganawar majalisar zartarwar kasar da shugaban kasar ya jagoranta.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta bayar, ta bayyana cewa, akwai gibin cefa biliyan 31.56 wato kimanin dala miliyan 63.12 a kasafin kudin da aka yiwa gyaran fuska maimakon gibin dala biliyan 50.177 wato kimanin cefa miliyan 100.35 a baya. Koda yake gwamnatin ta ce, za a cike gibin kasafin kudin ne daga tallafin ketare
Hukumomin kasar ta Mali sun lura da cewa, kasafin kudin na shekara ta 2013, zai mayar da hankali ne kan harkokin tsaro da rikicin siyasar da kasar ke fuskanta tun watan Maris din shekara ta 2012. Lamarin da ya dakusar da harkokin tattalin arziki tare da dakatar da samun tallafi daga manyan abokan huldar kasar.
Gwamnatin Mali dai ta ce, ta yanke shawarar gyara kasafin kudin kasar na shekara ta 2013 ne bayan dawo da huldar hadin gwiwa da wasu masu bayar da tallafin kudi, sakamakon aiwatar da taswirar shirin mika mulki da aka yi a watan Janairun shekara ta 2013.
Baya ga samun tallafin kudi daga abokan huldar ketare, har ila yau gwamnatin Mali tana fatan ganin kamfanonin hako ma'adinai su ma sun biya haraji, kuma gwamnatin ta tabbatar da cewa, za a yi amfani da albarkatun kasar wajen aiwatar da shirin na mika mulki wanda ke bukatar maido da harkokin tsaro da mulki a arewacin kasar bayan 'yan tawaye sun kwashe watanni suna mamaye da arewacin kasar, tallafin jin kai, tattaunawa da sasantawa kana da gudanar da babban zabe a kasar. (Ibrahim)