Sin tana fatan kasa da kasa za su ci gaba da taimakawa kasar Mali wajen kiyaye zaman lafiya
Bayan da kasar Chad ta sanar da janye sojojinta daga kasar Mali, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a ranar 16 ga wata a nan birnin Beijing cewa, yanzu ba a tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali ba, don haka akwai rawar da za a taka wajen tabbatar da ikon mallaka, cikakken yanki da kuma zaman lafiya a kasar Mali. A cewarta, kasar Sin tana fatan kasa da kasa za su ci gaba da mai da hankali da nuna goyon baya ga kasar Mali wajen taimakawa kasar don tabbatar da zaman lafiyarta.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan da kasar Faransa ta fara janye sojojinta daga kasar Mali a makon da ya gabata, shugaban kasar Chad ya bayyana a ranar 15 ga wata cewa, kasarsa za ta janye dukkan sojojinta daga kasar Mali. (Zainab)