Ya bayyana cewa, bisa hasashen da aka yi na yanzu, kusan 'yan miliyan 6,9 za su halarci wadannan zabubuka. Kuma takardun rajistan sunayen masu zabe za'a samar da su bisa tushen kidaya takardar zama dan kasa na RAVEC da kuma na rajistan fasahar zamani.
A lokacin da yake tabo maganar shiga zaben mutanen da suka kaura a cikin kasar, mista Coulbaly ya bayyana cewa lokacin sake duba rajista na musamman za'a amfani da shi domin rubuta sunayensu a cibiyoyi da runfunan zaben da suke son zuwa. Amma game da 'yan gudun hijira ya ce ana cigaba da tuntubar kasashen Mauritania, Nijar, Aljeriya da Burkina-Faso tare kuma da hukumar 'yan gugun hijira ta duniya HCR domin bullo da hanyoyin da za su taimakawa wadannan 'yan kasar Mali da aka tilastawa gudu nasu samu damar shiga wadannan zabubuka na watan Juli. (Maman Ada)