A cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin kakakin sa, Mr Ban Ki-moon ya nuna matukar damuwar sa cewa wadannan hare hare da ake kaiwa a 'yan kwanakin nan a Mogadishu yana nuna cewa manyan jami'an shari'a ne kawai ake hari da shi kan shi hukumar shari'ar,sai dai yana da imanin cewa duk wadannan hare hare ba zai dakushe kokarin da ake yi na karfafa tsarin dokar kasar ba.
Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba ne dai suka kai hari a kan mataimakin mai shari'ar gwamnatin kasar Ahmed Malim Sheikh Nur a Mogadishu babban birnin kasar a yammacin ranar alhamis din da ta gabata.
A cikin sanarwar Mr Ban ya mika ta'aziyyarsa ga Iyalan Ahmed Nur tare da jaddada kudurin majalisar na bada cikakken goyon baya da taimakon gwamnatin kasar ta Somaliya,hukumominta da kuma al'ummar kasar. (Fatimah Jibril)