Hafsan hafsoshin sojojin kasar Cote d'Ivoire Soumaïla Bakayoko ya bayyana a gun bikin tura sojojin a wannan rana cewa, kasarsa ta shirya tura rukunin sojoji masu samar da guzuri dake kunshe da sojoji 235 don shiga rundunar sojan bada taimako ta kasa da kasa a kasar Mali.
Rundunar sojan kasar Cote d'Ivoire ta fara ba da horo tare da kafa wannan rukunin soja mai samar da guzuri tun daga karshen watan Janairu na bana, kuma tawagar farko na rukunin ta tashi a ran 2 ga wata.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, rukunin sojan MDD dake kasar Cote d'Ivoire da sojojin kasar Faransa dake kasar sun horar da wannan rukuni na tsawon wasu 'yan watanni. (Zainab)