A wannan rana, a hedkwatar kungiyar EU, Traore ya yi shawarwari da shugaban kwamitin kungiyar EU Manuel Durão Barroso, bayan shawarwarin, Traore ya bayyana cewa, Mali za ta yi iyakacin kokarin tabbatar da fara babban zaben kasar daga ranar 28 ga watan Yuli na bana, shi kansa, da mambobin majalisar ministoci na gwamnatin wucin gadi, ba za su shiga babban zabe a matsayin 'yar takara ba.
Dalilin da ya sa Traore ya kai ziyara a kungiyar EU shi ne, domin halartar taron kasa da kasa game da ba da taimako ga batun kasar Mali da kungiyar EU da Faransa za su shirya a ranar 15 ga wata, taron da zai samu halartar shugaban kasar Faransa François Hollande da shugabannin kasashen yammacin Afrika da dama. Bayan shawarwarin, Barroso ya sanar da cewa, kungiyar EU za ta samar da kudin agaji da yawansa ya kai Euro miliyan 520 ga kasar Mali.
Tuni, a ranar 14 ga wata, yayin da ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ake shirin shirya taron shi ne, domin tattara kudin da yawansa ya kai Euro biliyan 1.9, da za a yi amfani da shi wajen aiwatar da shirin sake gina kasar Mali.(Bako)