Mataimakin shugaban ofishin tuntubar kasashen waje na ma'aikatar al'adu ta kasar Sin Sun Jianhua ya bayyana cewa, manufar wannan babban aiki da ake yi tsakanin Sin da mambobin kasashen kungiyar AL ita ce kafa wani sabon dandalin yin mu'ammalar al'adu tsakaninsu, har ma da kafa sabuwar alamar kasar Sin a fannin al'adu, ta yadda za a gabatarwa al'ummar kasashen Larabawa wata kasar Sin dake bayyana fasahar al'adu da ta kunshi gargajiya da na zamani tare.
Wannan ziyara ta kasance aiki mafi girma a fannin al'adu da Sin take yi tsakaninta da kasashen Larabawa tun lokacinn da aka kafa jamhuriyyar jama'ar kasar Sin, kuma za a yi irin wannan aiki ko wace shekara a mambobin kasashen kungiyar AL. Wasu kungiyoyin kasar Sin sun yi hadin kai domin gabatar da wannan aiki, ciki hadda ma'aikatar al'adu, ma'aikatar harkokin waje, hukumar yada labaru, hukumar kula da harkokin kayayyakin gargajiya masu daraja, kungiyar marubuta litattafai da sauransu. Yawan mahalarta shirin ya kai kimani dubu daga kungiyoyi da hukumomi kimanin 100 a kasar Sin. (Amina)