Nabil el-Araby ya nuna cewa, yana da muhimmanci ga Falesdinu da ta sami matsayin 'yan sa ido a MDD, domin wannan zai nuna amincewar kasa da kasa kan kasar Falesdinu, shi ya sa, samun matsayin ke da mihimmiyar ma'ana ga kasar.
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu, zamantakewar al'ummar duniya ta amince da kasar Falesdinu, inda zuwa yanzu har kasashe 132 mambobi ne na MDD sun amince da wannan, shi ya sa, ya kamata kasar ta dauki hakkinta a kungiyoyin duniya.
Nabil el-Araby ya kara da cewa, kasashen Larabawa sun cimma ra'ayi daya kan ba da goyon bayan ayyukan kasar Falesdinu.
Bisa labarin da aka samu, an ce, za'a tattauna batun Falesdinu a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da za a gudanar a ranar 12 ga watan Nuwanba a birnin Alkahira, da kuma taron kasashen Larabawa da kasashen Turai guda 27 da za a yi a ran 13 ga wata a birnin wato hedkwatar kungiyar tarayyar kasashen Larabawa. (Maryam)