Ranar Lahadi 15 ga wata a Alkahira babban birnin kasar Masar, an kira taron ministocin kungiyar kasashen Larabawa ta AL, inda aka cimma matsaya daya wajen gabatar da Nabil Elaraby ministan harkokin waje na kasar Masar da ya zama sabon sakataren kungiyar domin maye gurbin wani tsoho Amr Mahmoud Moussa
A gun taron, Elaraby ya ce, zai rike da wannan mukami yayin da kasashen Larabawa ke fuskantar mawuyancin hali, kamata ya yi, kasashen da suka halarci taron su hada kai domin warware wasu matsalolin kasashen Larabawa tare da daukar matakai da za su dace wajen sa kaimi ga ayyukan Larabawa. Amr Mahoud Moussa wanda ya sauka daga mukaminsa ya taya Elaraby murna.
An ba da labari cewa, Elaraby yana da shekaru 76 da haifuwa. Ya hau kan kujerar ministan harkokin waje na kasar Masar a ran 7 ga watan Maris na shekarar bana. Ya taba aiki a kotun shari'ar duniya, kwamitin dokar duniya na MDD, kwamitin neman diyya na MDD da sauransu. Ban da wannan kuma, ya taba zama mambar dindindin na kasar Masar dake MDD.(Amina)